Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya musunta rahotannin da ake yayatawa wai, kasar Sin ta biya bukatar kasar Amurka a yayin tattaunawar kasashen 2 kan tattalin arziki da ciniki.
Lu Kang wanda ya bayyana haka yau Jumma'a a nan Beijing, ya kuma bayyana cewa, labarin, jita-jita ne ke nan, kuma ana ci gaba da tattaunawar yadda ya kamata.
Rahotanni na cewa, wani jami'in Amurka ya bayyana jiya Alhamis cewa, a yayin tattaunawar da ake yi a wannan karo, kasar Sin ta ba da shawarar kara sayen kayayyakin Amurka, wadda darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 200 a ko wace shekara, shawarar da ta kusan yin daidai da shawarar da Amurka ta bayar a yayin tattaunawar farko. (Tasallah Yuan)