Sanarwar ta sheda cewa, bangarorin Sin da Amurka sun yarda da daukar matakai don rage gibin ciniki. Don biyan bukatun jama'ar kasar Sin a fannin sayen kayayyaki, da kara inganta tattalin arzikin kasar, bangaren Sin zata kara shigo da kayayyakin kasar Amurka da hidimomin da take samarwa. A bangare guda kuma, hakan zai taimakawa karuwar tattalin arzikin kasar Amurka, da kara guraben ayyukan yi a kasar.
Haka zalika, an baiwa kasar Amurka damar kara fitar da amfanin gona da makamashi. Inda aka ce, Amurkar zata tura wata tawaga zuwa kasar Sin don tattauna hadin gwiwar da za a yi a wannan fanni.
Ban da haka kuma, bangarorin 2 sun yarda zasu kara mayar da hankali kan kare ikon mallakar ilimi da fasahohi, sa'an nan zasu kara hadin kai a wannan bangare. Inda kasar Sin ta yi alkawarin daidaita wasu dokokinta a fannin kare ikon mallakar ilimi.(Bello Wang)