Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Jumma'a cewa, kasar Sin ta yi maraba da tabbacin tsaro da kasar Amurka a karon farko ta ce tana so bai wa kasar Koriya ta Arewa.
A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Lu Kang ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa gwiwar Amurka da Koriya ta Arewa na ganin sun kyautata fahimtar juna, su warware batutuwan da suke shafarsu ta hanyar yin tattaunawa, a kokarin kara azama kan daidaita batun zirin Koriya a siyasance tare.
A jiya Alhamis ne Donald Trump, shugaban Amurka ya ce, bai ce zai warware batun mukiliyar Koriya ta Arewa kamar yadda aka warware batun nukiliyar kasar Libya ba. Idan har shugaban Koriya ta Arewa ya amince ya dakatar da shirinsa na nukiliya, to Amurka za ta baiwa kasar tabbacin tsaro, kuma Koriya ta Arewa za ta samu kariya matuka. (Tasallah Yuan)