Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Laraba cewa, masu salon magana na cewa "Gaskiya ba ta bukatar kwalliya". Kaza lika kasashen duniya na da damar gano wanda ke tabbatar da tsarin ciniki cikin adalci a tsakanin bangarori daban daban, da kuma wanda ke tabbatar da ka'idojin ciniki na duniya. Kana ana iya gane wanda ke daukar matakan bada kariya ga cinikayya, da wanda ke saka takunkumi ga sauran sassa daga bangare daya. Mr. Geng ya ce yana fatan kasar Amurka, za ta daina zargin sauran sassa, kasancewar ita ce ke da hannu a al'amarin.
Geng Shuang ya yi nuni da cewa, yanzu haka an shiga muhimmin lokaci na farfado da tattalin arzikin duniya. Yana kuma fatan kasar Amurka za ta dauki alhakinta, na kasancewa kasa ta farko mai ci gaban tattalin arziki a duniya, da taka rawar da ta dace a duniya. (Zainab)