Jiya Lahadi ne shugaba Donald Trump na kasar Amurka, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, kasarsa da kasar Sin na kokarin ganin kamfanin ZTE na kasar Sin dake kera na'urorin sadarwa, ya dawo da gudanar da harkokinsa. Ya ce, ya umarci ma'aikatar kasuwancin Amurkar da ta warware wannan matsala.
Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yau Litinin a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yaba wa kyakkyawan ra'ayin Amurka kan batun kamfanin na ZTE, tana kuma tuntubar Amurka yadda ya kamata, game da matakai filla-filla da za a dauka. Sa'an nan kuma, kasashen 2 suna tuntubar juna, dangane da wasu batutuwan da Amurka take mai da hankali a kan su. (Tasallah Yuan)