Yau Jumma'a a nan Beijing Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana matukar rashin jin dadin kasar Sin da kin amincewa da kalaman da jami'an kasar Amurka suka furta kan yankin Taiwan, inda ya kuma kalubalanci kasar Amurka da ta martaba ka'idar "kasar Sin daya tak a duniya", tanade-tanaden da ke cikin sanarwoyi guda 3 da kasashen Sin da Amurka suka bayar cikin hadin gwiwa, da alkawarin da Amurka ta yi, ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin dangane da huldar da ke tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan.
Rahotanni na cewa, Marco Rubio, dan majalisar dattijai ta Amurka ya bayyana a yayin taron ba da shaidu da kwamitin harkokin wajen majalisar dattijan Amurka ya shirya a ranar 16 ga wata cewa, watakila kasar Paraguay za ta dakatar da huldar jakadanci a tsakaninta da Taiwan. Sa'an nan a kwanan baya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce, yadda Jamhuriyar Dominican ta dakatar da huldar jakadanci a tsakaninta da Taiwan bai taimaka wajen kiyaye kwanciyar hankali a yanki ba. (Tasallah Yuan)