Mahukuntan kasar Sin sun bayyana cewa, sun samu takardar gayyata daga sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin, wadda ke gayyatar mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, da ya ziyarci Amurka domin ci gaba da tattaunawa, kan harkokin da suka jibanci tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Wata sanarwa da ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar a Larabar nan, ta ce Sin ta amshi wannan gayyata, kuma jami'in zai ziyarci kasar Amurka a lokacin da ya dace. Sanarwar ta kara da cewa tuni wakilan kasashen biyu suka fara tattaunawa mai ma'ana.
Mr. Liu He shi ne wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mamba a kwamitin koli na hukumar siyasa ta JKS, wanda ke jagorantar bangaren Sin, a tattaunawar da kasar ke yi da tsagin gwamnatin Amurka, game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki.(Saminu Alhassan)