Tsohon mashawarcin jakada kan harkokin tattalin arziki na Afirka ta Kudu dake kasar Sin Yusuf Adam ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne matakan da kasar Amurka ta dauka za su haddasa barazana ga yanayin tattalin arzikin duniya, bai kamata kasashen duniya su yi shiru kan wannan batu ba, sai a dauki matakan tinkarar matsalar cikin sauri.
Wani malamin jami'ar Kenyatta ta kasar Kenya ya bayyana cewa, kasar Sin tana aiwatar da harkokinta yadda ya kamata ta fuskar babban kuskuren da kasar Amurka ta yi. Kuma Sin ta nuna aniyarta ta kiyaye tsarin cinikin duniya, lamarin da ya sa kaimi ga kasa da kasa wajen yin adawa da matakin kariyar cinikin da kasar Amurka ta yi, da kuma bada tabbaci ga kasa da kasa wajen karfafa dunkulewar kasa da kasa a fannin tattalin arziki. (Maryam)