Sin tana da kwarin gwiwa da kuma kwarewar magance kalubaloli a fannin fasahohinta
Wani jami’in ofishin kula da hakkin mallakar fasahohin kasar Sin SIPO ya sanar da cewa, kasar tana da kwarin gwiwa da kuma kwarewar tunkarar duk wasu kalubaloli da suka shafi fannin hakkin mallakar fasahohinta wato (IPRs).
Zhang Zhicheng, shugaban sashen kula da hakkin mallakar fasahohin IPR, karkashin hukumar SIPO ta kasar Sin, yace nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin cigaban fasaha ba wai ta kwafe su ko kuma ta sato fasahohin daga wani waje bane, sai dai irin jajurcewa da namijin kokarin da al’ummar sinawa suka nuna a wannan fanni.
Bincike mai lamba 301 da Amurka tayi game da kasar Sin na zarginta da satar fasahohi da fannin kirkire kirkire zargi ne marar tushe, inji mista Zhang.
A cewar jami’in, bunkasuwar da kamfanonin kasar Sin suka samu da yadda suke iya gogayya da kasa da kasa ya samo asali ne sakamakon yadda kasar ta zuba makudan jari a fannin kirkire kirkire, da irin karfin takarar da masana’antun kasar ke dashi a fannin ingancin tsarin masana’antu da kuma kwararrun ma’aikata masu tarin yawa da suke dasu, kana da irin fasahohin zamani da kamfanonin kasar ke amfani dasu.
Zhang yace, kasar Sin ta riga ta samu kima a ciki da wajen kasar sakamakon inganta tsarin kiyaye hakkin mallakar fasahohinta, kuma hakan ya bata damar samun karuwar kamfanonin wajen dake sha’awar yin rejista a kasar.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku