Cikin sharhinsa, Liu Xiaoming ya bayyana cewa, a kwanakin baya, Amurka ta ci zarafin kasar Sin, inda ta zarge ta da satar fasaha daga wajenta, bisa bincike mai lamba 301 da ta yi. Sannan, ta zargi kasar Sin da tilasta wa kamfanoninta su mika fasahohinsu gare ta, lamarin da ya sa, Amurkar za ta fara kara haraji kan kayayyakin da Sin ke sayar mata.
Dangane da wannan lamari, Mr. Liu ya ce, Amurka ta musunta ci gaban da kasar Sin ta samu cikin shekarun baya bayan nan a fannin karfafa fasaharta, wanda ya ce, zargi ne da ba shi da tushe, wanda kuma ya keta dokokin WTO, lamarin da ya nuna irin halin Amurka na son kai, da kuma kariyar ciniki da take yi a halin yanzu.
Haka kuma, jakada Liu ya ce, kasar Sin tana dukufa wajen sabunta fasahohi domin neman ci gaba, kuma tana tsayawa tsayin daka wajen kare ikon mallakar fasaha. Ya ce, an samu ci gaba kwarai bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Burtaniya da ma kasashen Turai baki daya, a fannonin sabunta fasahohin zamani, da kuma kare ikon mallakar fasaha.
Bugu da kari, ya ce, an cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin sassa daban daban a fannonin kare dokoki da manufofin da cinikayya da musayar bayyanai da kuma ba da horo da sauransu. Inda ya ce, a nan gaba kuma, kasar Sin za ci gaba da yin hadin gwiwa da kasa da kasa domin kare ikon mallakar fasaha da kuma sabunta kimayya da fasaha ta yadda za a kara tallafawa al'ummomin duniya baki daya. (Maryam)