Babban sakataren taron dandalin tattaunawar Asiya na Boao, Zhou Wenzhong, ya ce babu mafita wajen ba da kariya kan harkokin ciniki, inda ya ce hakika, Amurka na fuskantar matsalar tattalin arziki, amma shugabanta Donald Trump, bai lalubo bakin zaren warware matsalar ba.
Zhou Wenzhong, ya bayyana haka ne da yammacin jiya Lahadi, yayin taron manema labaru da aka shirya kan taron dandalin tattaunawar Asiya ta Boao.
A cewar mista Zhou, manyan matsalolin tattalin arziki da Amurka ke fuskanta su ne, yin sayayya fiye da kima da kuma rage yawan kudaden da aka ajiye a banki, inda ya ce duk da haka, ba da kariya kan harkokin ciniki ba zai iya warware matsalolin ba. (Tasallah Yuan)