Bayan Donald Trump ya hau kan ragamar mulkin Amurka, ya fara nuna kiyaya ga kasa da kasa, kamar bincike mai lamba 232 da ma'aikatar kasuwancin kasar ta yi kan kayayyakin karafa da na gorar ruwa da ake shigar da su kasarsa daga ketare, sa'an nan, ya kuma bukaci yin gyare-gyare kan yarjejeniyoyin ciniki da kasarsa ta riga ta kulla da kawayenta. Zuwa yanzu kuma, ya yi bincike bisa doka mai lamba 301 domin cin zarafin kasar Sin. Amma kasar Sin ta nuna aniyarta ta mai da martani kan dukkan matakai mara kan gado da Amurka za ta dauka a kanta. Kasar Sin ta bayyana cewa, idan gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump tana son ci gaba da wannan harka, to ita ma ba za ta ji tsoro ba, kuma tabbas za ta mai da martani daidai da na Amurka. (Maryam)