Yau Jumma'a, jaridar People's Daily ta kasar Sin ta wallafa wani bayani wanda ya nuna cewa, kalaman da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fidda, dangane da duba yiwuwar kara harajin da yawansa ya kai dala biliyan 100, kan karin wasu hajohin da Sin ke sayarwa Amurka, ya tayar da hankulan kasuwannin kasar Amurka da farko, lamarin da ya haddasa matukar raguwar darajar hannayen jari a kasuwannin Dow Jones da Nasdaq.
A hannu guda, kasar Sin ba za ta ji tsoron hakan ba, sabo da ko wane irin takunkumin cinikayya da kasar Amurka ta kakaba wa kasar Sin, tabbas Sin za ta mai da martani cikin sauri daidai da na Amurkan.
Sannan Sin za ta ci gaba da yin amfani da tsarin warware takkadamar bisa dokokin WTO domin kare hakkokinta. (Maryam)