Dangane da kalaman Shugaba Donald Trump na Amurka, na duba yiwuwar kara harajin da yawansa ya kai dala biliyan 100, kan karin wasu hajojin da Sin ke sayarwa Amurka, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya bayyana yau Jumma'a cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar fansa, tare da daukar sabbin matakai, ko da mene ne kasar Sin za ta sadaukar, za ta tsaya tsayin daka kan kare moriyarta, da ta jama'arta.
Gao Feng ya ce kasar Sin ta bayyana ra'ayinta a fili kan batun tattalin arziki da ciniki a tsakaninta da Amurka, wato ba ta fatan shiga yakin ciniki, amma kuma ba ta jin tsoron hakan.
Kakakin ya kara da cewa, Amurka ce ta haddasa matsalar ciniki a tsakaninta da kasar Sin a wannan karo. Kaza lika Amurka ta dauki ra'ayin kashin kai, na yunkura matsawa wasu masu ra'ayin cudanya da sauran rukunoni da yawa. Har ila yau Amurka na neman ba da kariya ga ciniki ta hanyar matsawa masu ra'ayin yin ciniki cikin 'yanci a duniya.
A hannu guda kasar Sin za ta ci gaba, da kara bude kofarta ga kasashen waje da yin gyare-gyare a gida, za ta kuma kiyaye tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban, a kokarin kara azama kan yin ciniki da zuba jari a duniya cikin 'yanci da sauki. (Tasallah Yuan)