Hua Chunying ta bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba shiryawa, lokacin da aka bukaci ta yi tsokaci game da rahotanni dake cewa, Amurka da Sin sun jima suna zantawa da juna kan batutuwa da suka jibanci cinikayya. Kana Amurka ta bukaci Sin da ta rage harajin da take sanyawa kan ababen hawa kirar Amurka, ta kuma kara yawan wasu kayan latironi da take saya daga kasar, kana ta fadada damar da take baiwa kamfanonin Amurka a kasuwanninta.
Jami'ar ta ce tattaunawa da cimma matsaya tare, su ne kadai hanyoyi da za su ba da damar gina ginshikin mutunta juna, da samar da daidaito da adalci, maimakon wani bangare ya rika gabatar da bukatar sa ta hanya mai kama da tursasawa.
Da ta tabo batu game da sauye sauye da kasar Sin ke gudanarwa a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje kuwa, Hua ta ce Sin ta cimma manyan nasarori cikin shekaru 40 da suka gabata, kuma za ta ci gaba da bude kofofin ta tare da zurfafa gyare gyare.
Ta ce Sin na aiki matuka, domin samar da kasuwa mai cike da adalci ga hajojin ta na gida da ma wadanda ke shigowa daga ketare, ta yadda za a ci gaba da takara mai tsafta ba tare da nuna bambanci ba.(Saminu Alhassan)