Cikin sanarwar, an kuma bayyana cewa, kasar Sin ta dukufa matuka domin warware matsalolin dake shafar harkokin tattalin arziki da ciniki dake tsakaninta da Amurka, bisa ka'idojin mutunta juna da kuma cimma moriyar juna, inda ta kuma ba da shawara masu kyau domin bunkasar hadin gwiwar Sin da Amurka bisa wannan fanni. Kuma, kasar Sin ba ta son tada yakin ciniki, amma kuma ba ta tsoron yakin, saboda tana da karfin fuskantar da dukkan kalubalen da batun ya shafa.
Ta kara da cewa, Idan Amurka ba ta tsayar da kudurin yin yakin ciniki, kasar Sin za ta dauki matakai yadda ya kamata domin kare moriyarta.
Tabbas ne, kariyar ciniki masu tsari da kasar Amurka ta dauka za ta haddasa wa mutane da kamfanoni da kasuwar sha'anin kudin kasar ita kanta illa, kana, za ta yi barazana ga tsarin cinikin kasa da kasa da kuma yanayin zaman karko na tattalin arzikin duniya.
Shi ya sa, kasar Sin take fatan Amurka za ta tsayar da matakan cinikayya masu tsauri da ta dauka, tare da mai da hankali kan tsai da kudurorin da abin ya shafa, domin kada a jefa dangantakar ciniki dake tsakanin kasar Sin da Amurka cikin mawuyacin hali, lamarin da zai bata yanayin tattalin arziki da ciniki na kasar Amurka ita kanta. (Maryam)