Jiya Laraba, wani masanin kasar Sin ya ce, kamata ya yi huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta shiga sabon zamani na yin hadin gwiwar neman samun nasara tare.
Wang Wen, shugaban gudanarwa na kwalejin nazarin harkokin kudi na jami'ar jama'ar kasar Sin ta Chongyang ya kara da cewa, kasashen 2 su ne mafiya karfin tattalin arziki a duniya suna iya taimakawa juna ta fuskar masana'antu.
Mista Wang ya fadi haka ne a yayin wani taro da babban kwamitin kasuwanci na kasar Sin mai zaman kansa dake kasar Amurka ya shirya, yana kuma wakiltar kamfanonin kasar Sin a kasar Amurka. Mista Wang ya yi nuni da cewa, kasar Sin na dacewa da yin hadin gwiwa da ita domin samun moriyar juna. Haka kuma, hanya daya kacal da Sin da Amurka za su bi domin samun wadata tare ita ce inganta mu'amala a tsakaninsu. (Tasallah Yuan)