in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun tattauna kan batun zirin Koriya da kuma dangantaka a tsakanin kasashensu ta wayar tarho
2018-03-10 13:20:22 cri

Shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump, sun gana ta wayar tarho a jiya, dangane da yanayin da zirin Koriya ke ciki da kuma dangantakar dake tsakanin kasashensu.

Da yake magana, shugaba Xi Jinping ya ce ya yi maraba da muradin Shugaba Trump na warware batun zirin Koriya a siyasance, yana mai fatan Amurka da Jamhuriyar Al'ummar Koriya za su fara tattaunawa nan ba da dadewa ba domin samun kyakkyawan sakamako.

A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce batun yana samun kyautatuwa a baya-bayan nan, inda ya ce taro tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa ya dace da muradun bangarorin biyu, yana mai fatan za a cimma masalaha kan batun nukiliyar.

Shugaba Trump ya kara da cewa, Shugaba Xi ya yi gaskiya da ya matsa kan a warware rikicin bisa hawa teburin sulhu, yana mai bayyana godiyar Amurka game da muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka wajen warware batun na zirin Koriya, kuma a shirye Amurkar take ta karfafa tuntuba da hadin gwiwa da kasar Sin dangane da batun.

Shugabannin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan dangantakar dake tsakanin kasashensu.

Xi Jinping ya yi fatan yunkurinsu bisa mutuntawa da moriyar juna, zai inganta hadin gwiwa tsakaninsu kan harkokin tattalin arziki domin moriyar kasashen biyu, tare da habaka dangantakar dake tsakaninsu a wannan sabuwar shekara.

Trump ya ce dorewar dangantaka tsakanin shugabanin biyu zai bada gagarumar gudummuwa wajen ciyar da dangantakarsu gaba. Yana mai cewa, Amurka na daukar batun hulda da hadin gwiwa da muhimmanci, kuma a shirye take ta hada hannu da kasar Sin wajen kyautata huldar dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China