Yau Alhamis Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sake nanata matsayin kasar Sin game da rikicin tattalin arziki da ciniki a tsakaninta da kasar Amurka a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya ce, Sin da Amurka sun dade suna tuntubar juna dangane da yadda za a daidaita wannan takaddama. Sin na fatan kasashen 2 za su daidaita rikicin ta hanyar yin hadin gwiwa yadda ya kamata. Lu Kang ya kuma jaddada cewa, abubuwan da suka faru a tarihi sun shaida cewa, yakin ciniki ba abu ne da ya dace da muradun kowane bangare ba. Don haka kasar Sin za ta tsaya kan kiyaye hakkokinta. (Tasallah Yuan)