Wani jami'in ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta ce, kasar za ta dauki dukkan matakan da suka dace na kare hakkokinta da moriyata.
Da yake mayar da martani a jiya, ga rahotannin da ke cewa, Amurka za ta fitar da sakamakon binciken sashe na 301 da ta yi kan kasar Sin, wannan jami'in ma'aikatar ya ce, babu yadda za a yi, kasar Sin ta nade hannu tana kallo ana yi wa moriyarta da hakkokinta illa.
A watan Augustan 2017 ne Amurka ta fara wani bincike kan fasahohi da yayyata fasahar kasar Sin karkashin sashe na 301 na dokar cinikayya ta 1974.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, nan ba da dadewa ba gwamnatin Amurka za ta sanar da sakamakon binciken tare da sanya matakai masu tsauri a kan kasar Sin.
Game da binciken na sashe 301, jami'in ya ce, kasar Sin ta bayyana matsyinta sau da dama, inda ta nuna rashin amincewarta da irin wadannan shingayen cinikayya masu tsauri na Amurka.
Tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979, cinikayya tsakaninsu ta karu har sau 232, inda jimillar jari tsakaninsu ya zarce dala biliyan 230. (Fa'iza Mustapha)