Kasar Sin ta bayyana cewa, ta yi maraba da labari mai dadi game da sanarwar da kasashen Amurka da Koriya ta Arewa suka bayar na yin tattaunawa kai tsaye a tsakanisu.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan Jumma'ar nan, a nan birnin Beijing, ya ce wannan wani ci gaba da ya dace game da batun nukiliyar Zirin koriya, kuma kasar Sin ta yaba matuka da wannan mataki kana tana goyon bayan kokarin da sassan da wannan batu ya shafa suka yi game da magance batun ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.
Rahotanni na cewa, shugaba Donald Trump na Amurka ya amince ya gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a watan Mayun wannan shekara bisa gayyatar shugaba Kim.(Ibrahim)