Jakadan kasar Sin dake Amurka Cui Tiankai ya bayyana cewa, hadari ne babba a ce wata kasa za ta yi fito-na-fito da kasar Sin.
Jakadan na Sin wanda ya bayyana hakan yayin wata liyafa da aka shirya ranar Talata a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ta Amurka albarkacin bikin Bazara na al'ummar Sinawa, ya ce, bai kamata ma a yi tunanin cewa, kasar Sin wadda ke bin turbar neman ci gaba cikin lumana za ta yi fito-na fito da kasar Amurka. Haka kuma babban hadari ne a ce wata kasa za ta nemi yin fito-na-fito da kasar Sin.
Ya ce, mafarki ne a ce wai, za a iya amfani da wani mataki na siyasa ko al'ada a canja yanayi ko kwayar halittar gado na kasar Sin. Ya ce, bai dace a canja sigogin dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Amurka ba, kuma muddin dai akwai takara, to bai dace a yi maganar fito-na-fito ba.
Jakadan na Sin ya ce, duk da bambance-bambance da wasu 'yan matsaloli da sassan biyu suke fuskanta nan da can, kasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa don ganin an gano bakin zaren warware wadannan batutuwa. Yana mai cewa, abu mafi muhimmanci shi ne muradun dake shafarsu.(Ibrahim)