Yayin ganawar tasu, mista Yang ya waiwayi ziyarar da shugaba Donald Trump ya yi a kasar Sin a watan Nuwamban shekarar data gabata, inda ya ce shugaban Amurka ya cimma ra'ayi daya tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping, cewa kasar Sin da kasar Amurka suna da moriyar bai daya, da nauyin dake bisa wuyansu, a kokarin tabbatar da samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da walwala a duk duniya. Kana huldar dake tsakanin kasashen 2 zata yi tasiri ga yanayin siyasar duniya. Ganin haka ya sa mista Yang ya bayyana burinsa na ganin bangarorin Sin da Amurka sun cigaba da kokarin aiki tare, da kara kokarin mu'amala da musayar ra'ayi tsakaninsu, da gudanar da wasu tarurrukan musayar ra'ayi tsakanin manyan kusoshin kasashen 2 wadanda ake saran gudanarwa a bana lami lafiya, da habaka hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin soja, da harkar shari'a, da dakile fataucin miyagun kwayoyi, da al'adu, da dai makamantansu, da kokarin daidaita sabanin ra'ayi don kara karfafa dankon zumunci dake tsakanin kasashen 2.
A nasa bangaren, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, huldar dake tsakanin Amurka da Sin nada muhimmanci matuka, saboda haka ya ce akwai bukatar aiwatar da daidaiton da ya cimma tare da shugaban kasar Sin mista Xi Jinping yayin da suka yi ganawa a birnin Beijing na kasar Sin a bara. A cewarsa, kasar Amurka na son hadin kai tare da kasar Sin, don kara kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)