Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai yau Alhamis, ya ce ayar dokar wadda Amurkar ta sanya cikin kasafin kudinta na shekarar 2018 , ta sabawa manufar "kasar Sin daya tak a duniya" da kuma manufofin sanarwar hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, kuma hakan tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin.
Lu Kang ya ce, ko shakka babu kasar Sin ba ta goyon bayan wannan mataki, kuma tuni ta gabatar da kokenta ga gwamnatin Amurka.
A ranar Talata ce shugaba Trump ya sanya hannu kan wannan ayar doka, inda wasu sassanta suka amince sojojin ruwan Amurka da yankin Taiwan na kasar Sin su rika ziyartar juna.(Ibrahim)