Mr. Lu ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa. Hakan dai ya biyo bayan zartas da wasu dokoki guda biyu da majalissar wakilan Amurka ta yi, don gane da alakar Amurkan da yankin Taiwan.
Dokokin dai sun hada da wadda ke karfafa gwiwar jami'an diflomasiyyar sassan biyu su rika ziyartar juna, da kuma wadda ke umartar sakataren wajen Amurka, da ya mayarwa yankin na Taiwan matsayin wakiliya 'yar kallo a hukumar lafiya ta duniya WHO.
Lu Kang ya ce wadannan dokoki biyu sun ci karo da manufar kasar Sin ta kasancewa daya tak a duniya, da kuma wasu yarjeniyoyin hadin gwiwa 3 da Amurka ta kulla da Sin. Daga nan sai ya jaddada adawar kasar Sin da wannan mataki na neman shiga harkar cikin gidan kasar da Amurka ke neman yi.
Har ila yai Mr. Lu ya nanata burin kasar Sin, na ganin cewa Amurka ba ta tura jami'an ta yankin na Taiwan ba, kana ta kaucewa baiwa 'yan awaren yankin na Taiwan duk wata dama, ta cika burin su na neman samun 'yancin kan yankin. Bugu da kari jami'in ya yi fatan cewa, Amurka za ta kare martabar alakar ta da Sin a mataki na kasa da kasa. (Saminu)