A jawabinsa yayin bikin rufe shirin, Kwamanda Zhang Jian na bangaren sojojin 'yantar da jama'a na kasar Sin ya bayyana cewa, musayar dabarun ayyukan jin kai tsakanin sojojin sassan biyu zai kara karfafa amincin sama da shekaru 20 dake tsakanin sassan biyu.
Zhang ya ce, a shirya sojojin kasar Sin suke su yi aiki da takwarorinsu na Amurka domin zurfafa hadin gwiwa a bangarorin da suka shafi ayyukan jin kai da rigakafin aukuwar bala'u, a kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya da shiyya-shiyya.
Shi ma da yake jawabi, kwamandan sojojin Amurka mai kula da yankin Fasifik Robert Brown, ya bayyana fatan cewa, Amurka da Sin za su ci gaba da hada karfi da karfe don karfafa musayar bayanai tsakanin sojojin sassan biyu, da kara yin tattaunawar masanan sassan biyu, da gudanar da horo kan ayyukan jin kai da rigakafin aukuwar bala'u, a wani mataki na inganta karfinsu na ayyukan jin kai da ceto.
A ranar 13 ga watan Nuwamba ne, aka fara shirin samun horo na tsawon mako guda da ya gudana a sansanin horas da sojoji dake jihar Oregon ta Amurka.(Ibrahim)