Hukumar FAO ta tabbatar da kasashe 19 dake fama da karancin abinci cikin dogon lokaci
Jiya Litinin, a yayin babban taron hukumar abinci da ayyukan gona ta MDD wato FAO da aka yi a birnin Roma na kasar Italiya, babban sakataren hukumar Jose Graziano da Silva ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2015, adadin mutane masu fama da karancin abinci yana ci gaba da karuwa, a halin yanzu, an tabbatar da kasashe guda 19 wadanda suke fama da karancin abinci cikin dogon lokaci.
Bisa rahoton da hukumar ta fitar, an ce, yankin arewa maso gabashin Nijeriya, da Somaliya, da Sudan ta Kudu da kuma kasar Yemen suna fuskantar babban kalubalen barkewar bala'in yunwa a kasashen, kuma harkar za ta shafi mutane kimanin miliyan 20. (Maryam)