in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin shiga da aka samu daga masu sayar da abinci ta kafar intanet a Sin ya zarce dala biliyan 50 a 2016
2017-03-20 11:08:03 cri

Kungiyar masu sana'ar abinci ta kasar Sin ta ce, kudin shiga da aka samu daga masu sayar da abinci ta kafar intanet ya zarce yuan biliyan 350 kwatankwacin dala biliyan 50.7 a shekarar 2016, kimanin kashi 10 na jimilar kudin shiga da ake samu daga sana'ar.

Hada hadar cinikayyar abinci ta intanet na samun tagomashi a sassan kasar Sin, sai dai kuma, rashin kwararan matakai na sanya ido kan masu cinikayyar abincin na haifar da karancin inganci ta fuskar wannan hidima ga al'umma.

Domin daidaita wannan matsala, hukumar kula da ingancin abinci ta kasar Sin, ta wallafa wani kundi na sa ido kan harkokin sayar da abincin, inda ta bayyana cewa, dole ne masu sayar da abinci ta kafar intanet su samu shaguna da kuma shaidar ba su damar gudanar da sana'ar.

Shugaban hukumar Bi Jinquan, ya bukaci masu sayar da abinci da ba su suka sarrafa ba, su kara zage damtse wajen daukar masu dafa abinci aiki.

Wani shehun malami a jami'ar nazarin aikin gona ta kasar Sin Zhu Yi, ya ce kundin zai tabbata da cewa, masu sana'ar na kwarewa, kuma su gudanar da aiki yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China