Daraktan WFP Valerie Guarnieri, ya furta hakan ne ga manema labarai a hedkwatar hukumar UNICEF dake birnin New York.
Dukkannin hukumomin biyu UNICEF da WFP suna bukatar kudade domin agazawa mutanen da matsalar ta shafa a yankunan.
To sai dai kuma, a wani labarin makamancin wannan, alamu na gwada cewa ana fuskantar jan kafa wajen samar da kudaden da za'a gudanar da aikin bada agajin, kamar yadda mai magana da yawun MDD, Stephane Dujarric, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a a jiya Talata ya ce ana bukatar tallafin kudi kimanin dalar Amurka biliyan 4.4, domin hukumar ta samu zarafin gudanar da ayyukanta na agazawa mutanen dake fuskantar karancin abinci a sakamakon rikice rikice a kasashen da suka hada da arewa maso gabashin Najeriya, Somalia, Sudan ta kudu da kasar Yemen, kuma masu bada agajin sun tara dala miliyan 984 wato kashi 21 na adadin kudaden da ake bukata. (Ahmad)