in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta baiwa yankunan da fari ya shafa a Kenya gudummawar buhunan abinci 100,000
2017-06-22 09:30:37 cri

A jiya Laraba ne kasar Sin ta mika kashin farko na gudummawar buhunan abinci kimanin dubu 100 don rabawa yankunan dake fama da matsalar yunwa a kasar Kenya.

Da yake jawabi yayin bikin mika kayayyakin da ya gudana a birnin Nairobin, jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa, ya bayyana cewa, gudummawar shinfakar wani bangare ne na alkawarin da mahukuntan na Sin suka yi na ba da tallafin buhuna 450,000 na abincin ga masu fama da wannan matsala.

Jakada Liu ya ce, za a kawo ragowar tallafin abincin cikin watan Yuni, da tsakiyar watan Yulin, yayin da kashin karshe zai iso cikin watan Agustan wannan shekara.

Mr Liu ya ce, kasar Sin tana tausayawa yanayin karancin abincin da al'ummar ta Kenya suka shiga sakamakon matsalar canjin yanayi, wadda ta yi illa ga bangaren aikin noma. Ya ce, har kullum a shirye al'ummar Sinawa suke su agazawa takwarorinsu na kasar Kenya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A nata jawabin, babbar sakatariya a sashen kula da da ayyuka na musamman na kasar Kenya Josepheta Oyeila Mukobe ta yabawa taimakon da Sinawa suka baiwa al'ummar Kenya da ke fama da matsalar yunwa, sakamakon matsalar farin da ta aukawa dimbin jama'a.

Tallafin kayan abinci da Sin ta bayar wadda darajarsa ta kai dala miliyan 22.5 wani bangare ne na tan 21,366 na kayan abincin da za a rabawa mutanen da ke fama da matsalar yunwa a sassa daban-daban na kasar ta Kenya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China