in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka suna kokarin daidaita rikicin karancin abinci
2017-04-11 12:30:11 cri

Jiya Litinin aka kaddamar da babban taron kungiyar Red Cross da ta Red Crescent ta kasashen Afirka karo na 9 a Abidjan, hedkwatar mulkin kasar Kwadibuwa, inda wakilan kasashen Afirka mahalarta taron za su tattauna kan batun game da yadda za a warware rikicin karancin abincin da kasashen Afirka ke fama da shi.

Mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar kasa da kasa ta kungiyar Red Cross da ta Red Crescent ya bayyana a yayin bikin kaddamar da taron da cewa, yanzu wajibi ne a warware rikicin karancin abincin da kasashen Sudan ta Kudu da Najeriya da Somaliya ke fama da shi, kana kasashen Kenya da Habasha su ma suna fuskantar rikicin karancin abinci mai tsanani.

A yayin wannan taron, shugaban kungiyar Red Cross ta kasar Kwadibuwa shi ma ya bayyana cewa, mahalarta taron za su tattauna kan batun game da yadda za a samar da taimako ga gwamnatocin kasashen Afirka ta hanyar daukar hakikanan matakai, domin isar da taimakon kai tsaye ga mutanen da suke bukata, a sa'i daya kuma, kungiyar Red Cross da ta Red Crescent za su taka muhimmiyar rawa a fannin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China