Kungiyar tarayyar Afrika AU ta ce, za ta taimakawa kasashe mambobinta wajen rage dunbun hasarar kayan abincin da ake yi bayan kammala rore su.
Kwararren mai ba da shawara ga sha'anin rage hasarar abinci na kungiyar AU Cephas Taruvinga, ya fadawa taron koli kan aikin gona a Nairobi cewa, nahiyar Afrika tana yin hasarar tsakanin kashi 20 zuwa 40 cikin 100 na dukkan amfanin gonar da aka noma a duk shekara.
Taruvinga ya ce, AU za ta taimakawa kasashen Afrika wajen samar da hanyoyin da za su rage yawan hasarar abinci da kasashen na Afrika ke yi bayan kammala girbe amfanin gonar.
Taron na tsawon kwanaki hudu, ya gayyato masu bincike, da masana dabarun mulki, da jami'an gwamnatoci, da kuma bangarori masu zaman kansu a duk fadin nahiyar ta Afrika, domin dubawa da kuma nazartar hanyoyin da za'a rage yawan hasarar abinci a fadin nahiyar.
Taruvinga ya ce, matsalar hasarar abincin tana matukar haifar da koma baya ga burin nahiyar Afrika na samar da wadataccen abinci. Ya ce, idan Afrika ta magance matsalar hasarar abincin da take yi, to ba ta bukatar shigo da kayan abinci daga kasashen waje.
A halin da ake ciki, nahiyar ta shirya wani tsari na rage hasarar abincin da take yi da kashi 50 bisa dari nan da shekarar 2025.(Ahmad Fagam)