Sanarwar da Kungiyar AU ta fitar a jiya Jumma'a ta ruwaito cewa, taron na yini biyu da ya gudana a ranakun 13 da 14 ga watan nan a hedkwatar Tarayyar Afrika dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya samu halartar masana daga kungiyoyin raya yankunan Afrika daban daban da hukumomin MDD da masu bincike.
Ana gudanar da binciken na gano yadda makaman ke yaduwa ne karkashin jadawalin taron kwamitin sulhu da wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU da ya gudana ranar 24 ga watan Afrilun 2014 mai taken 'kawar da bindigogi, tubalin wanzar da zaman lafiya a Afrika ya zuwa shekarar 2020", wanda ya nemi hukumar ta AU ta yi nazari kan yadda haramtattun makamai ke shiga da yaduwa a cikin nahiyar, sannan ta mika sakamakon binciken.
Wannan shi zai ba AU da kungiyoyin raya yankuna da kasashe mambobi su kare yaduwar haramtattun makamai zuwa yankunan dake fama da rikici, da aiwatar da dabaru da matakai da za su dace da manufofin kungiyar AU na kawar da bindigogi a nahiyar kawo shekarar 2020. (Fa'iza Mustapha)