Smail Chergui, kwamishinan lura da zaman lafiya da tsaro na AU ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar dake da nasaba da bikin ranar kiyaye kan iyaka ta Afrika, ya yaba da irin nasarorin da aka samu cikin shekaru 10 a shirin kula da kan iyakoki na Afrika (AUBP).
Ya bukaci kasashen mambobin na AU, da kasashen shiyyar masu raya tattalin arziki, da sauran masu ruwa da tsaki, da su dauki dukkan matakan da suka dace wajen cimma nasarar shirin na AUBP da kuma fadada yadda ake aiwatar da shi.
Manufar shirin na AUBP shi ne, domin kare afkuwar tashe tashen hankula, sannan da lalibo bakin zaren warware dukkan wata takaddama da ta shafi rikicin kan iyakoki, wanda abin takaici ne saboda fuskantar yawan rikice rikicen kan iyakokin da ake samu a 'yan shekarun nan, musamman sakamakon cigaban aikin hako danyen mai da aikin hakar ma'adanai a yankunan, inji Chergui.
Kwamishinan ya yi kira da'a kara kokarin cimma karin nasarorin magance halin tabarbarewar tsaro da ake ciki a halin yanzu, kasancewar matsalolin sun fi kamari ne a kan iyakokin kasashen.(Ahmad Fagam)