A jiya Litinin ne Kungiyar ECOWAS ta gudanar da wani biki da ya jibanci cika shekaru 42 a harabar hedkwatar AU a Addis Ababa babban birnin Habasha, mai taken 'ECOWAS a shekaru 42: waiwaye da buri".
A jawabinta, Amira Al-Fadil kwamishinar kula da walwalar al'umma ta AU, ta jadadda cewa, ECOWAS ta cimma nasarori a fannoni daban-daban.
Amira Al-Fadil, ta ambato hadin kan yankin da tabbatar da tsarin demokaradiyya da siyasa da wanzar da zaman lafiya a matsayin wasu daga cikin muhimman bangarori da kungiyar ta samu nasara cikinsu.
Kwamishinar ta AU, ta kuma bayyana ECOWAS a matsayin abar koyi ga sauran kungiyoyin yankuna a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)