A yayin taron kungiyar ta AU karo na 27 da aka gudanar cikin watan Yulin da ya gabata a birnin Kigali ne, kasashe mambobin kungiyar suka dorawa shugaba Paul Kagame na kasar Rwandan nauyin jagorantar yadda za a aiwatar da gyare-gyaren da kungiyar ta gabatar, ta yadda kungiyar za ta cimma nasarar manufofin da ta sanya a gaba na inganta rayuwar al'ummomin nahiyar.
A watan Janairun ne dai dukkan shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar suka amince da gyare-gyaren da kungiyar ta gabatar a yayin ganawarsu a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rwandan ta fitar ta bayyana cewa, shugaban kasar Paul Kagame zai karbi bakuncin taron ministocin harkokin wajen kasashen Afirka 54 da na jakadun kasashen Afirka da ke aiki a kungiyar AU domin tattauna hanyoyin da za a aiwatar da wadannan gyare-gyare.(Ibrahim)