Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour, ya ce taron hadin gwiwar tsakanin kasashen biyu ya shafi batun siyasa da tsaro wanda kungiyar ta AU ta kafa kwamiti don gayyatar kasashen na Sudan da Sudan ta kudu, wanda shugaban kwamitin aiwatar da shirin zaman lafiya na (AUHIP), Thabo Mbeki, ya shirya ganawa da su domin tattauna batutuwa da suka jibinci shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
Mr Mbeki ya ce, AUHIP za ta gudanar da taron ne a Addis Ababa tsakanin ranakun 8 da 9 ga watan Mayu domin tattauna batutuwa da suka shafi aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya, ciki har da batun shata kan iyakoki, da yankunan da aka cimma daidaito kansu da batun samar da matsugunnai, da dakile yaduwar makamai.
Kasashen Sudan da Sudan ta kudu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2013 a Addis Ababa domin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka riga aka rattaba hannu kansu, daga ciki akwai batun gaggauta janye dakaru a kan iyakokin kasashen biyu, da kuma shata yankuna bisa amincewar kasashen biyu.
Daga cikin sharrudan yarjejeniyar akwai batun shata kan iyakokin da tattalin arzikin kasashen biyu. Sai dai yarjejeniyar ba ta warware matsalar yankin nan na Abyei mai arzikin mai ba.
Batun rikicin kan iyakoki shi ne babban al'amari dake haifar da tada jijiyar wuya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu. (Ahmad Fagam)