Taken Taron wanda aka yi a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na Habasha, tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Rwanda dake kasar, shi ne 'tunawa da kisan kare dangi na Rwanda - yaki da akidar kisan kare dangi - kara inganta nasarorinmu'
Tarayyar Afrika ta ce manufar taron ita ce, tunawa da rayukan da aka yi asararsu a Rwanda a shekarar 1994, da nuna goyon baya da kauna ga wadanda suka kubuta tare da kara inganta hadin kai, domin tabbatar da makamancin al'amarin ba zai kara faruwa a kasar Rwanda ba, ko wata kasa a Afrika ko duniya baki daya.
Da yake jawabi yayin taron, mataimakin shugaban kungiyar Thomas Kwasi Quartey, ya jadadda cewa, ana gudanar da taron ne duk shekara a ranar 7 ga watan Afrilu, domin tunawa da wandanda al'amarin ya rutsa da su, tare da sake sabonta kudurin al'ummar nahiyar Afika na kare 'yancin dan Adam. (Fa'iza Mustapha)