A cewar kasafin kudin kasar Rwanda na 2017/2018, gwamnati za ta mai da hankali wajen inganta ababen more rayuwa da kayakin da ake sarrafawa a cikin gida a shekarar kudi ta badi.
Ministan harkokin kudi da tattalin arziki na kasar Claver Gatete ne ya bayyana haka a jiya Alhamis, lokacin da yake gabatar da kasafin kudin gwamnati na shekarar kudi ta 2017/2018, a gaban majalisar dokokin kasar, inda jimilar kudin ya kai dala biliyan 2.5.
Claver Gatete ya ce tsarin tattalin arziki da ke kunshe cikin kasafin na 2017/2018, zai fi mai da hankali ne kan zuba jari domin inganta kayakin more rayuwa da kayakin da ake sarrafawa a cikin gida.
Ya ce kara zuba jari kan kayakin more rayuwa da kayakin da ake sarrafawa a cikin gida, zai gaggauta cimma manufar kasar ta kai wai matsakaicin mataki na samun kudin shiga.
Kasafin na 2017/2018 ya nuna Karin da aka samu daga dala biliyan 2.3 a shekarar 2016/2017 zuwa dala biliyan 2.5. (Fa'iza Mustapha)