Louise Mushikiwabo ta bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai game da dangantakar diflomasiyya tsakanin Rwanda da kasashen duniya daban-daban.
Tun a shekarar 2010 ne dangantaka ta yi tsami tsakanin Afrika ta Kudu da Rwanda, a lokacin da Kigali ta zargi Afrika ta Kudu da ba masu laifin kasarta mafaka.
A shekarar 2014 ne kuma, kasasehen biyu suka yanke huldar dake tsakaninsu, inda kowacce ta kori jami'an diflomasiyyar dayar daga kasarta, bayan rashin jituwa da aka samu da zargin cewa, jami'an tsaron Rwanda na aikata laifuka a Afrika ta Kudu.
Afrika ta Kudu ta kori jami'an diflomasiyyar Rwanda uku, inda a wani mataki na mai da martini, Rwanda ta kori jami'an diflomasiyyar Afrika ta kudu 6. Sai dai, dukkansu sun kyale zaman jakadun juna a kasashensu.
Amma, Mushikiwabo ta ce tuni kasashen biyu suka amince da daidaita dangantaka a tsakaninsu, ciki har da yin cinikayya da juna da kuma karfafa huldar diflomasiyya. (Fa'iza Mustapha)