Ta ce kasar Seychelles wadda ita kadai ce ta baiwa 'yan Afirka damar shiga ba tare da neman takardar Visa ba, ba ta fuskantar wata barazana ta tsaro. A ganin ministar harkokin wajen kasar ta Rwanda, budewa juna kofar musaya tsakanin kasashen nahiyar ba abun da zai haifar, illa gaggata dunkulewar nahiyar waje guda.
Kaza lika ministar ta ce babu wata hanya da kasashen Afirka za su bi, ta bunkasa cinikayya, da zuba jari, tare da bunkasa tattalin arzikin juna, muddin ba su amince su bude kofofinsu ga juna ba. Don haka ya yi kira ga mahukuntan nahiyar, da su zakulo hanyoyin inganta dokoki, wadanda za su baiwa 'yan Afirka damar shiga kasashen juna ba tare da wani tarnaki ba. (Saminu Hassan)