Gwamnatin Rwandan tana duba yiwuwar bada lada da bada kariya ga duk mutumin da ya tona asirin jami'an gwamnati da aka samu suna aikata ba daidai ba, ko wasu hukumomi da aka samu da laifin almundahana wajen gudanar da ayyuka, inji wani babban jami'in gwamnatin kasar.
A cewar minista mai kula da gyaran kundin tsarin mulkin kasar Evode Uwizeyimana, ya bayyana cewa, dokar fallasa masu aikata laifukan wadda tuni tana gaban majalisar dokokin kasar domin yi mata kwaskwarima, za ta tabbatar ana boye sunayen masu tonon sililin, kana za'a basu kariya da kuma basu lada bisa ga ayyukan fallasar da suka yi.
Uwizeyimana ya ce, suna kokarin bankado masu aikata rashawa da masu yin amfani da mukamansu wajen arzurta kansu daga cikin baitulmalin gwamnati, kuma hakan na haifar da barazana wajen tabbatar da tsaron kasa da zaman lafiyar kasar.(Ahmad Fagam)