Masanan sun bayyana hakan ne, yayin wani taron karawa juna sani mai lakabin Dot Finance Africa ko (DFA) a takaice, wanda ya gudana a birnin Kigali na kasar Rwanda.
Yayin taron da aka bude a jiya Alhamis, mahalartan sa sun jaddada muhimmancin amfani da fasahohin sadarwa, domin fadada tare da inganta hada hadar cinikayya a nahiyar Afirka.
Da yake tsokaci game da wannan lamari, babban jagoran cibiyar TagPay mai samar da hidimar harkokin cinikayya ta na'urorin tafi da gidan ka Mr. Yves Eonnet, ya ce kamata yayi cibiyoyin hada hadar kudi na Afirka, su bullo da hanyoyin shigar da biyan kudade cikin tsare tsaren su na raya tattalin arziki.
Kasar Rwanda ce ke karbar bakuncin taron DFA na yini biyu dake gudana a wannan karo. Taron ya kuma tara manyan kusoshi a fannin hada-hadar kudi sama da 500 daga kasashen Afirka daban daban, da ma wasu yankuna na kasashen duniya.(Saminu Alhassan)