Taron wanda aka fara a ranar Asabar da ta gabata a sansanin sojoji na Galo dake gabashin kasar Rwanda, ya hada da sojojin kasashen Algeriya, Angola, Benin, Burkina Faso, Chadi, Masar, Nijer, Rwanda, Senegal, Afrika ta kudu, Sudan, Tanzaniya da Uganda.
Taron ba da horo na sojin karo na 3 mai taken "Utulivau Afrika III", za a gudanar da shi ne daga ranar 20 zuwa 31 ga wannan wata na Maris.
Ana gudanar da taron ne karkashin shirin horas da dabarun kai daukin gaggawa na Afrika wato ACIRC a takaice.
ACIRC, shiri ne na musamman tsakanin kungiyar tarayyar Afrika AU da kasashen duniya masu aikin sa kai, da nufin taimakawa kungiyar ta AU wajen kai daukin gaggawa da zarar aka samu barkewar tashin hankali a nahiyar Afrika.
A shekarar 2013 ne aka kaddamar da wannan shirin a matsayin shiri na wucin gadi kafin Afrikar ta samu takamammiyar rundunar wanzar da tsaro wacce za ta yi aiki yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)