Haka zalika, wani jami'in gwamnatin kasar da bai fadi sunansa ba, ya bayyana wa manema labarai cewa, Amurka ta kori mutanen 72 ne saboda matsalar karancin takardun shaidar zama da sauran wasu abubuwa masu alaka da wannan, inda ya ce tuni mutanen suka isa birnin Nairobi a jiya da safe, sannan, su ma 'yan kasar Somaliya guda 67 za su tafi Mogadishu, babban birnin kasar.
A yayin babban zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata, Donald Trump ya yi alkawarin cewa, bayan ya rike ragamar mulkin kasar, zai hana shigar 'yan cin rani ba bisa ka'ida ba, yayin da kara mai da hankali ga 'yan cin rani da suka riga suka shiga kasar ba bisa doka ba.
Kuma bayan ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Amurka ne, har sau biyu, ya ba da umurni a hukumance na hana wasu 'yan kasashen ketare shiga Amurka. (Maryam)