Sanarwar da fadar White House ta fitar, ta ce da yake ganawa da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov a birnin Washinton DC, Trump ya ce akwai yiwuwar fadada dangantakarsu ta fuskar warware rikice-rikice a yankin gabas ta tsakiya da sauran wurare.
Ganawar ta zo ne a lokacin da ake tsaka da samun rashin fahimta tsakanin Amurka da Rasha kan wasu batutuwa da suka hada da rikicin Syria da na Ukraine da kuma batun fadada kungiyar tsaro ta NATO.
Yayin ganawar ta jiya Laraba, Trump ya jaddada bukatar kasashen biyu su yi aiki tare wajen kawo karshen rikicin Syria.
Bayan ganawar, Sergei Lavrov ya shaidawa manema labarai cewa, Donald Trump ya bayyana sha'awar da yake da ita, ta inganta hulda da Rasha ta yadda kasashen biyu za su amfana. (Fa'iza Mustapha)