Yayin taron manema labarai na kulla-yaumin, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce galibin wadanda aka ceto 'yan Afrika ne, amma kuma akwai adadi mai yawa na 'yan kasar Bangladesh.
A cewar hukumar IOM, daga farkon shekarar nan kawo yanzu, mutane 900 ne suka mutu a cikin teku, kuma kashi 90 daga cikinsu na kan hanyarsu ne ta zuwa Italiya daga kasar Libya.
Har ila yau, ta yi kiyasin cewa, 'yan cirani 20,000 ne ke tsare a wasu cibiyoyin tsare mutane da basa bisa ka'ida.
Dujarric ya ce hukumar ta MDD ta jadadda yin kira ga Tarayyar Turai da gwamnatoci su ceci rayuwar jama'a.
Cikin kwanaki uku daga ranar 14 zuwa 16 ga wannan watan, masu tsaron teku na Italiya da jiragen ruwan kasuwanci da na kungiyoyi masu zaman kansu, sun ceto jimilar 'yan cirani 8, 360 a Bahar Rum. (Fa'iza Mustapha)