A jiya Asabar ne rundunar sojojin ruwan kasar Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, jirgin ruwan yakin Amurka da jiragen saman yaki ke sauka a kansa mai suna USS Carl Vinson CVN-70 da sojojin ruwan Koriya ta Kudu suka yi wani atisayen soja na hadin gwiwa a gabashin tekun zirin Koriya. Kafofin watsa labaru na kasar Koriya ta Kudu sun ruwaito sojojin ruwan kasar na bayyana cewa, tun daga karfe 6 na yammacin jiya agogon wurin ne aka fara atisayen soja na hadin gwiwar. Bisa halin tsaron da ake ciki, an yi atisayen sojan ne don kara karfin sojan kawancen Koriya ta Kudu da Amurka.
Rahotanni na nuna cewa, watakila za a kai har mako mai zuwa ana yin atisayen sojan, kuma atisayen ya sahfi tinkarar harin makamai masu linzami, ciki har da nema, da tare makamai masu linzami dake shawagi a sama, da dai sauransu.
A kwanakin baya ne jirgin ruwan yaki na CVN-70 da rundunar kiyaye tsaro ta ruwa ta kasar Japan suka yi horo na hadin gwiwa a yammacin tekun Pasifik. (Zainab)