Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen ta bayar a jiya ta ce, bangarorin biyu za su tattauna kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya a gabashin kasar Ukraine, da aiwatar da yarjejeniyar Minsk wajen warware batun Ukraine a dukkan fannoni.
Game da batun Syria kuwa, ministocin za su tattauna kan yadda za a sassauta matsanancin yanayin da kasar ke ciki, da samar da gudummawar jin kai ga fararen hula, da shirya warware matsalar da take fuskanta a siyasance.
Yayin jawabin da ya yi a ma'aikatartasa ranar 3 ga wata, Tillerson ya ce babu amincewa da juna tsakanin Amurka da Rasha a halin yanzu, kuma dangantakar da ke tsakaninsu na cikin wani hali mafi tsanani tun lokacin cacar baki. (Zainab)