Haka kuma, a ranar 6 ga wata, aka gabatar da cikakken bayani kan batun gina yankunan tsaro hudu a kasar Syria ta shafin intanet na ma'akatar harkokin wajen kasar Rasha. Kuma an cimma ra'ayi daya kan wannan bayanin da aka fito a yayin taron shawarwarin neman sulhu kan batun Syria da aka yi a birnin Astana a ranar 3 da ranar 4 ga watan nan da muke ciki, kana, za a fara yin amfani da bayanin tun daga ranar 6 ga wata.
Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Amurka ta aike da sabbin ma'aikata masu sa ido da su halarci sabon taron shawarwarin, inda suka yi hadin gwiwa da kasashen Rasha, Iran, Turkiya da kuma Syria da dai sauran kasashen da abin ya shafa wajen warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa.
Bugu da kari, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, kasar Amurka ita ma tana goyon bayan kafa yankunan tsaro a kasar Syriar. (Maryam)